A wani sako da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce bayaga mutane 23 da suka mutu, akwai kuma wasu sama da 40 da suka samu raunuka.
Kasuwar da aka kai harin dai, na kusa da babban sansanin rundunar sojojin RSF da ke birnin Khartoum, waɗanda sojojin ƙasar ke fafata wa da su a yakin basasan da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.
Tun a ranar Juma'a da ta gabata ne dai ake gwabza kazamin faɗa a kusa da birnin na Khartoum, wanda yawancinsa ke ƙarƙashin ikon RSF, inda sojoji suka yi ta luguden wuta a tsakiyar birnin da kuma kudancin sa ta hanyar amfani da jirage sama.
Shaidun gani da ido sun ce a ranar Asabar da ta gaba, sojojin Sudan sun doshi birnin na Khartoum daga Omdurman, lamarin da yayi sanadiyar ɓarkewar wani rikici.
Tun a tsakiyar watan Afrelun shekarar bara ne dai, rikici ya ɓarke a Sudan tsakanin sojojin ƙasar da ke ƙarƙashin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa da ke jagorantar RSF Mohamed Hamdan Daglo.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce akalla mutane dubu 20 aka kashe a rikicin, sai dai wasu alkaluma na nuna cewa adadin ya kai dubu dari da 50.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI