Harin wanda kungiyar Al-Shabaab ta dau alhakinsa kamar dai yada kungiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ya sa hukumomin wannan kasa sanar da daukar matakan kare kai daga hare-haren kungiyar ta Al Shebab.
Ministan lafiya na Somalia Ali Haji Adam ya shaidawa manema labarai cewa: “Jimillar wadanda suka mutu da hukumomi suka tabbatar sun kai 37.
Wadanda suka tsira daga harin sun ce bayan da dan kunar bakin waken ya tashi bam wasu mutane sun bude wuta a bakin tekun, suna neman su "kashe duk wanda za su iya."
An sanya maharan a matsayin makiya, kalmar da hukumomin Somaliya ke amfani da su wajen ayyana 'yan kungiyar.
Yan lokuta bayan wannan kazamin hari,asibitoci sun fuskanci karanci jinni,wanda ya kai su ga shigar da kira ga jama’a na ganin sun bayar da gudunmuwar jini domin jinyar wadanda suka jikkata, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.
Wani abin lura da shi,shine lokacin da harin ya afku,an lura cewa mutane da dama ne suka ziyarci bakin tekun Lidoo.
Shugaba Hassan Cheikh Mohamoud ya bayana alhini sa a shafinsa na X da kuma daukar alkawalin kira taron gaggawa tareda kasancewar Firaministan kasar da manyan jami’an tsaron kasar ta Somalia.
Daga kasashen waje,sakonni alhini kama daga Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka ta AU, Moussa Faki Mahamat ,
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce ya yi matukar bakin ciki da yadda 'yan Somaliya ke ci gaba da fuskantar wannan munanan ayyukan ta'addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI