Wani haɗarin motar safa ya laƙume rayukan mutane 28 a Habasha

Wani haɗarin motar safa ya laƙume rayukan mutane 28 a Habasha

Rahotanni sun ce wata motar Safa ce maƙare da fasinja ta afka cikin ruwa daga saman gada, wanda ya kai ga mutuwar mutanen 28 baya ga jikkatar wasu 19, haɗarin da tuni mahukuntan Habasha suka tabbatar da faruwarsa.

Wani saƙo da mahukuntan na Addis Ababa suka wallafa shafinsu na Facebook ya bayyana cewa haɗarin ya faru ne a yankin Wolaita mai tazarar kilomita 400 daga kudancin birnin Addis Ababa fadar gwamnatin ƙasar.

Har zuwa yanzu dai babu cikakkun alƙaluma kan yawan mutanen da ke cikin motar, sai dai mahukuntan na Addis Ababa sun ce ana ci gaba da laluben mutanen da ake kyautata zaton sun nutse ne a cikin ruwan.

Wasu hotuna da aka wallafa a shafin Facebook sun nuna yadda motar gabaki ɗayanta ta tsunduma ruwan yayinda wundunanta suka farfashe haka zalika saman rufinta.

Bayanai sun ce motar ta jujjuya akan titi tare da buguwa da ginin gadar gabanin faɗawa cikin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)