
Kamfanin dillancin labaran na Fana, ya bayyana cewa mai kula da harkokin zirga-zirgar ababen hawa na shiyyar Wollega ta Gabas, Asnake Mesfin ya bayyana musu cewa, bas ɗin ta taso ne daga Shambu da ke yammacin kasar zuwa Addis Ababa babban birnin kasar.
Asnake ya ce wasu mutane 42 sun jikkata kuma ya kuma kara da cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.
A wannan wuri dai bayanai sun yi nuni da cewa ana yawan samun munanan hadurran ababen hawa a kasar ta Habasha, bisa rashin bin ƙa’idojin tuƙi, da kuma rashin ba a kula da motoci.
Akalla mutane 71 ne suka mutu a karshen watan Disamba a yankin kudancin Sidama lokacin da wata babbar mota dauke da fasinjoji ta fada cikin kogi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI