
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta bayyana cewa dubban mutane ne aka tilastawa ficewa daga muhallansu a jihar yammacin Equatoria ta Sudan ta Kudu bayan shafe makwanni cikin tashin hankali da aka fuskanta a garin Tambura da kewaye.
Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu UNMISS, ta bayyana cewa zaman lafiya ya dawo yankin, wanda ya sanya mazauna yankunan da suka tsere komawa kusa da sansanin UNMISS na wucin gadi.
A yayin da Kanar Shams Sittique, babban jami'in soji na UNMISS, ya ce tawagar na ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da kokarin shawo kan matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI