Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna yiwuwar ɓangaren adawa ya lashe zaɓen Ghana

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna yiwuwar ɓangaren adawa ya lashe zaɓen Ghana

Tsohon shugaban ƙasar ta Ghana Mahama mai shekaru 65, da mataimakin shugaban ƙasa mai ci Bawumia dake da shekaru 60, su ne manyan ƴan takara a zaɓen shugaɓancin ƙasar da za’a gudanar ranar 7 ga watan disambar bana, domin maye gurbin shugaban ƙasar mai ci, Nana Akufo-Addo da zai sauka a watan janairun shekarar 2025 bayan kammala wa’adinsa na 2 a matsayin shugaban ƙasar Ghana.

Duk da cewa akwai wasu Ƴan takarar 11, amma binciken da kafar Global InfoAnalytics dake birnin Accra ta gudanar, ya nuna yadda Mahama na jam’iyyar NDC ke da kashi 52 yayin da Bawumai na NPP, yake biye masa baya da sama da kashi 41 cikin 100 a ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a.

Binciken ya ce mafi yawan masu zaɓen sun fi damuwa da a samar musu da yanayin tattalin arziƙi mai kyau, ayyukan yi, ilimi da ababen more rayuwa.

Mahama dai ya mayar da hankali matuƙa kan ababen more rayuwa lokacin da ya jagoranci ƙasar tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017, yayin da ya fuskanci suka kan ƙarancin wutar lantarki da taɓarɓarewar tattalin arziƙi, an kuma zargi gwamnatinsa da cin hanci da rashawa, duk da cewa ba a taba zargin Mahama kai tsaye ba.

Bawumia, masanin tattalin arziƙi, kuma tsohon ma’aikacin babban bankin ƙasar ne yake wa jam’iyyar NPP mai mulki takara, jam’iyyar da ta yi fama da matsalar tattalin arzikin Ghana mafi muni a tsawon lokaci.

Ghana ce ƙasa ta biyu a duniya dake samar da cocoa, kuma ta gaza biyan mafi yawan bashin da ake binta na dala biliyan 30 da ta karɓo daga kasashen waje a shekarar 2022, bayan da ta kwashe shekaru tana karɓowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)