Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) zai aika da allurai kimanin miliyan 220 na sabon nau'in kwayar cutar Corona (Covid-19) zuwa kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Afirka.
A cewar bayanin da UNICEF ya yi, an sanya hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Janssen Pharmaceutica NV na kasar Beljiam don isar da allurar riga-kafin Johnson&Johnson miliyan 220 ga nahiyar nan da karshen 2022.
Yarjejeniyar, wacce ke hango isar da allurai miliyan 35 a karshen wannan shekarar, ta ba da damar samar da alluran riga-kafi miliyan 180 idan ana bukatar hakan.
A wata sanarwa da aka fitar bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, shugabar UNICEF Henrietta Fore ta bayyana cewa babu daidaito a samun alluran riga-kafi a duniya, kuma suna ci gaba da ba da goyon bayan samar da damar yin allurar riga-kafi a nahiyar Afrika.