Ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun zafafa kai hare-hare a Burkina Faso - HRW

Ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun zafafa kai hare-hare a Burkina Faso - HRW

Babbar jami’in bincike ta ƙungiyar a yankin Sahel Ilaria Allegrozzi  ce ta bayyana hakan a cikin sakamakon binciken da suka gudanar daga watan Faburairun wannan shekara zuwa yanzu, wanda ya nuna cewa ƴan bindigar sun kai munanan hare-hare 7 da suka yi sanadiyar mutuwar fararen hula aƙalla 128, lamarin da ta ce ya sabawa dokokin kare hakkin dan adam na duniya.

Mun fuskanci damuwa game da ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso, ƙungiyoyin sun yi kisan gillar ga mazauna kauyuka da masu ibada da kuma raba mutane da muhallansu, wanda hakan ya saba wa hakkin dan Adam.

A rahotan da ƙungiyar ta fitar a Laraban nan da ke cike da shaidu daga wajen waɗanda suka fuskanci cin zarafin, sun bayyana yadda ƴan bindigar ke bi gida-gida wajen yiwa mutane gisan gilla da yanke musu harsuna ko kuma yiwa mata fyaɗe, idan har suka ƙi amince wa bukatarsu ta miƙa wuya.

Sai dai ƙungiyar ta ce alƙaluman da ta tattara, basu ƙunshi na mutane dari zuwa dari 4 da aka kashe a wani hari da aka kai a ranar 24 ga watan daya gabata, a yankin Barsalogho da ke tsakiyar ƙasar ta Burkina Faso ba.

Burkina Faso dai na daga cikin ƙasashen yankin Sahel da ke fama da matsalar masu iƙirarin jihadi, domin ko a ranar Talata, sai da wasu majiyoyi suka sanar da cewar da dama daga cikin mazauna Arewacin garin Djibo, da ke zaman tudun muntsira, sun tsere daga gidajensu a ranar 14 ga wannan watan, bayan da aka basu umarnin hakan ko kuwa su fuskanci hukuncin kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)