Ƙungiyar ta'addanci ta Katiba Macina a Mali ta yi tsokaci kan faɗaɗa hare-harenta zuwa sassan Afrika
Wannan jawabi kaɗan ne daga cikin tattaunawar da fitattacen ɗan Jaridar RFI sashen Faransanci Wassim Nasr yayi da Hamadoun Kouffa shugaban tsagin Katiba Macina na ƙungiyar JNIM da ke da alaƙa ta kai tsaye da ƙungiyar Al-Qaeeda da ta addabi yankin Sahel da hare-hare.
Bayan kwashe tsahon shekaru biyu yana bibiya don ganin ya sami damar tattaunawa da shi, a ƙarshe dai Hamadoun Kouffa ya amsa tambayoyi 14 cikin 17 da ɗan jarida Wassim Nasr ya aike masa, sai dai kuma don gudun baiwa ƴan ta’adda damar yaɗa Farfaganda RFI ba zata wallafa muryarsa ba, sai dai kaɗan daga cikin tambayoyin da ya amsa har da batun faɗaɗar da Rasha ke yi a ƙasashen Afrika.
Hamadoun Kouffa ya ce babu wani ci gaba da Rasha ta samar a yankin sahel game da sha’anin tsaro, illa ma dai sake harzuka jama’a wanda ya baiwa ƙungiyarsa ta JNIM damar sake ɗaukar matasa.
Kouffa ya ce har yanzu yana nan kan bakansa, na gujewa afkawa fararen hula haka kawai, kuma ba zai kaiwa ƙungiyoyin bada agaji hari ba, matuƙar basu bari anyi amfani da su wajen cimmusu ba.
Ko da aka tambaye shi kan yadda yaransa ke kaiwa fararen hula hari, ya dora alhakin hakan kan hare-haren ba gaira ba dalili da dakarun Rasha na Wagner da kuma sojojin Mali ke kaiwa sansanonin su baji ba gani, yana mai cewa duk da yana ƙyamar kaiwa fararen hula hari, amma ba zai iya hana yaransa ɗaukar fansa ba.
To sai dai kuma ya yaba ƙwarai kan hare-haren da yaran Jafar Dicko shugaban ƙungiyar JNIM da ke Burkina Faso kan hare-haren da suke kaiwa jami’an tsaro da fararen hula a wasu lokutan a ƙasar.
Kouffa ya kuma bayyana aniyarsu ta faɗaɗa hare-harensu zuwa ƙasashen Ghana, Togo da kuma Jamhuriyar Benin, yana mai cewa a shirye suke su shiga tattaunawa da shugabannin ƙasashen Mali, Nijar da kuma Burkina Faso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI