A cikin wani faifan sauti da ke yawo a kafafen sada zumunta kungiyar mai alaka da Al-Qaeda, ta yi ikirarin sace shugaban addini.
Shaidu sun ce mayakan ɗauke da muggan makamai sun tare tawagar motocin Sheikh Amadou Hady Tall a wani ƙauye da ke kusa da kan iyakar ƙasar, yayin da yake komawa daga wasu tarukan addinin da ya halarta a ƙasar Mauritaniya.
Sheikh Hady na da ra'ayin sassauci saɓanin ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadin da ke yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI