Ƙungiyar ECOWAS ta sallami ma'aikata 'yan asalin Nijar da Mali da Burkina Faso

Ƙungiyar ECOWAS ta sallami ma'aikata 'yan asalin Nijar da Mali da Burkina Faso

Sanarwa ɗaga ECOWAS na ɓayyana cewa an miƙawa ma’aikatan takarɗun na sallama a hukumance,wanda hakan ke tabbatar da cewa sun ɗaina aiki da ƙungiyar bayan da ƙasashensu da suka hada da Mali, Nijar da Burƙina Faso suka daina  zama mambobin ƙungiyar tun daga ranar 29 ga watan Janairun 2025.Rahotanni na ɓayyana cewa akalla ma’aiƙata 130 suka fito daga ƙasashen.

Zauren taron kungiyar ECOWAS Zauren taron kungiyar ECOWAS REUTERS - Marvellous Durowaiye

Ƙungiyar ta ECOWAS ta kafa wani kwamiti da ke da alhakin tattaunawa da ƙasashen na Nijar,da Burkina Faso da Mali kan "tsarin ficewa", wanda ya shafi 'yancin zirga-zirgar jama'a da kayayyaki, da wani yanayi na samar da hanyoyin kasuwanci, da na tattalin arziki, kayayyakin more rayuwa da raya kasa da kungiyar ta ECOWAS ta aiwatar ko kuma ta samar da ƙudade a ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso. Kasashen ukun sun ƙuma ce a shirye suke su tattauna da ƙungiyar ta ECOWAS tare da tabbatar ɗa cewa suna son ba ɗa fifiƙo ga muraɗun al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)