Ƙungiyar AU ta kira taron gaggawa don kawo ƙarshen rikicin Sudan

Ƙungiyar AU ta kira taron gaggawa don kawo ƙarshen rikicin Sudan

El-Fasher dai na daya daga cikin manyan birane 5 da ake yankin yammacin Darfur, kuma birni daya tilo da baya karakashin ikon mayakan RSF, tun bayan faro rikicinsu da sojojin ƙasar a tsakiyar watan Afrelun bara.

A ƙarshen mako ne dai mayakan RSF suka kaddamar da hare-hare a birnin da ke da yawan mutane miliyan biyu.

To sai dai shugaban ƙungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat, ya yi Allah wadai da yadda rikicin ke ci gaba da bazuwa.

Mahamat ya kuma kira taron gaggawa na kwamitin tsaro na ƙungiyar, don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a ciki da kuma wajen birnin na El-Fasher.

Dukkanin bangarorin da ke rikici da juna a Sudan, na zargin juna da aikata laifukan yaki, ciki har da kai hare-hare kan fararen hula da sata ko dakatar da isar kayan agaji.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi ƙiyasin cewar, adadin waɗanda aka kashe tun bayan faro rikicin ya kai dubu 20, sai dai ƙiyasin jakadan Amurka a ƙasar Tom Perriello ya nuna cewa kimanin mutane dubu dari da 50 ne aka kashe.

Rikicin ya kuma raba sama da mutane miliyan 10 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)