An kira babban taron na ƙasashen kudancin Afrika 16 ne bayan da ƴan tawayen M23 da Rwanda ke goyawa baya, suka kwace birnin Goma da ke gabashin Congo mai arziƙin albarkatun ƙasa a makon nan, a rikicin da aka shafe gwamman shekaru ana yi.
Sojojin Afrika ta Kudu 13 da na Malawi 3 aka kashe a rikicin na Congo, yawancinsu jami’an wanzar da zaman lafiya ne da ƙungiyar ta aike dasu yankin tun shekarar 2023.
Rwanda dai bata cikin ƙungiyar da shugaban ƙasar Zimbabawe Emmerson Mnangagwa ke jagoranta, sai dai jamhuriyar dimokraɗiyyar Congo na ciki amma babu tabbacin ko shugaba Tshisekedi zai halarci taron.
Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya bayyana rikicin a matsayin babbar matsala wanda ke barazana ga tsaro.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce sama da mutane dubu 2 ne suka jikkata, 45 suka mutu a birnin Goma, yayin da ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar barkewar cutuka irinsu ƙyandir biri, kwalara da ƙyanda saboda rasa muhallai da jama’a su ka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI