Hukumar raya ilimi, kimiyya da al’adu ta Majalisar ɗinkin duniya UNESCO ta ce abin damuwa ne matuƙa yadda ɓangarorin da ke yaƙin a Sudan suka lalata wuraren tarihi daban-daban da ke sassan ƙasar baya ga sace wasu kayakin tarihin ciki har da waɗanda ke killace a gidan adana kayan tarihi na ƙasar.
Sudan wadda ke fuskantar yaƙin fiye da shekara guda da rabi, a baya-bayan nan ne ɓangarorin da ke yaƙin suka fara farmakar wuraren tarihi wataƙila a wani yunƙuri na kawar da kayakin tarihin ɓangarorin ciki har da waɗanda aka killace ƙarƙashin kulawar UNESCO.
A cewar hukumar ta UNESCO, yanzu haka ta na sanya idanu kan halin da ake ciki a ƙasar bayan farmakar manyan gidajen adana kayakin tarihin da suka ƙunshi Khalifa House Meseum da ke Omdurman da kuma Nyala da ke kudancin Dafur baya ga uba uba babban gidan adana kayakin tarihi na ƙasa.
Babban gidan adana kayakin tarihin an Sudan da aka samar cikin shekarun 1970 na ɗauke da daɗaɗɗun kayan tarihi fiye da dubu 2 da 700 ciki har da wasu daga zamanin fir’aunonin Misra da kuma na ƙabilar Nubi mai dogon tarihi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI