A ranar Lahadi ne ƙasar Mali da ke yankin yammacin anhiyar Afrika ta sanar da yanke hulɗa da Ukraaine, biyo bayan kalaman hukumar leƙen asirin sojinta a kan yaƙin da aka gwabza arewacin Mali a ƙarshen watan Yuli.
A yayin wannan faɗa, ƴan tawayen Anzinawa sun ce sun kashe dakarun Wagner guda 84 da sojojin Mali 47, lamarin da ya kasance asara mafi muni da kamfanin sojojin hayar Wagner ta taɓa samu tun da ta shigo taimaka wa Mali wajen yaƙi da ta’addanci shekaru 2 da suka wwuce.
A wata sanarwa, ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta bayyana matakin Mali a matsayin abin takaici, wanda ta ɗauka ba tare da gudanar da binciken gaano ainihin gaskiyar lamari ba.
A cikin sanarwa, Ukraine ta ce ta yi watsi da zargin goyon bayan ayyukan ta’addanci na ƙasa-da-ƙasa, inda ta ce tana kallon matakin yanke hulɗa da ita a matsayin mai matuƙar tsanani.
Wannan rikicin diflomasiyya na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine ke neman ƙarin goyon bayan ƙasashen duniya a yaaƙin da ta ke da Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI