Uganda ta tura karin dakaru zuwa arewacin Jamhuriyar Congo

Uganda ta tura karin dakaru zuwa arewacin Jamhuriyar Congo

Sai dai rahotanni na cewa, mazauna yankin da suka tserewa rikicin, da dama daga cikinsu sun fara koma wa gidajensu.

Karin dakarun da Uganda ta tura arewacin Goma, zai kara yawan wadanda take da su a yankin, domin taimakawa dakarun gwamnatin shugaba Felix Tshisekedi, da ke fada da dakarun ‘yan tawaye akalla daga 4,000 zuwa 5,000, a cewar binciken Majalisar Dinkin Duniya.

Itama dai Rwanda akwai dakarunta da ta jibge a gabashin Congo, wadanda t ace suna aikin wanzar da zaman lafiya ne.

Uganda na taimakawa Congo wajen yakar masu dauke da makamai da suka addabi kasar tun daga sahekarar 2021, inda a halin take da dakaru tsakanin 1,000 zuwa 2,000 da ke fafatawa da ‘yan tawaye, karkashin shirin Operation Shujaa.

Sai dai mai Magana da yawun rundunar sojin Uganda, Felix Kulayigye ya musanta batun cewa kasarsa ta tura karin dakaru zuwa Congo, illa iyaka dai ta sauyawa wadanda t atura kasar ne wuraren aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)