UAE ta tsame kanta daga zargin taimakawa dakarun RSF a yakin Sudan

UAE ta tsame kanta daga zargin taimakawa dakarun RSF a yakin Sudan

Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce jiragen sama 122 ne suka kai kayayyakin agajin jin kai ga Amdjarass domin taimakawa 'yan Sudan da suka tsere daga yakin.

A makon da ya gabata, wani jami'in Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ya mika goron gayyata ga masu sanya ido na Majalisar Dinkin Duniya da su ziyarci wani asibiti da ke Amdjarass don su fahimci irin kokarin jin kai da UAE ta yi na taimakawa saboda ragewa al’uma radadin rikicin da ke faruwa a yanzu.

 

Rundunar RSF karkashin jagorancin Mohamad Hamdan Dagalo, ta shafe fiye da watanni tara tana yaki da sojojin kasar, karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan.

 

Yakin dai ya jefa kusan rabin al’umar Sudan cikin wani mawuyacin dake bukatar agaji, kuma sama da miliyan 7.5 sun bar gidajensu, a cewar MDD.

 

Dagalo a wannan yanayi da ake ciki ya mallaki mafi yawan yankin Darfur na yammacin Sudan da wasu sassan babban birnin kasar Khartoum.

 

Hakanan baya-bayan nan kuma kungiyar ta RSF ta kwace iko da Wad Madani, daya daga cikin manyan biranen kasar ta Sudan.

An zargi kungiyar da ke dauke da makamai, tare da kungiyoyin Larabawa masu dauke da makamai, da kashe mutane kusan 15,000 wadanda ba Larabawa ba daga kabilar Masalit a hare-haren da "ka iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil adama," a cewar rahoton.

 

A baya dai kungiyar ta RSF ta musanta zargin kuma ta ce duk wani sojanta da aka samu da hannu zai fuskanci shari'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)