Turkiyya ta yi Allah wadai da harin ta'addanci a Nijar

Turkiyya ta yi Allah wadai da harin ta'addanci a Nijar

Turkiyya ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa fararen hula a kauyen Toumour da ke yankin Diffa na Nijar.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar, an bayyana da matukar bakin ciki cewa mutane 28 sun rasa rayukansu kuma daruruwa sun jikkata a harin ta’addancin da aka kai wa fararen hula a daren 13 ga Disamba a kauyen Toumour da ke Kudu maso Gabashin kasar Nijar. Sanarwar ta bayyana cewar,

"Mun yi Allah wadai da wannan harin marasa gaskiya. Muna taya abokanmu da 'yan uwan mu ’yan Nijar da kuma gwamnatin kasar bakin cikin wannan mumunan lamarin. Muna fatan Allah ya ji kan waɗanda suka rasa rayukansu, kuma muna mika  ta'aziyyar mu ga iyalan mamatan. Muna yi wa masu raunuka fatan samun lafiya cikin gaggawa."

Kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta kai hari kan kauyen Toumour da ke yankin Diffa a daren 13 ga Disamba. A lamarin, mutane 28 sun rasa rayukansu kuma kusan gidaje 800 da wuraren aiki sun lalace. Gwamnatin Nijar ta aiyana zaman makoki na kwanaki 3 bayan afkuwar lamarin.

‘Yan Boko Haram sun kai hari a yankin Diffa a ranar 11 ga watan Disamba yayinda mutane 2 suka mutu a lamarin.

‘Yan kungiyar Boko Haram sun afkawa yankin tun a watan Fabrairun 2015.


News Source:   ()