Turkiyya ta yi Allah wadi da hare-haren ta'addancin da aka kai a ranar da ta gabata a Nijar.
A cikin sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar, an bayyana da matukar bakin ciki cewa sojoji 4 sun rasa rayukansu sannan sojoji 8 sun jikkata a harin ta’addancin da aka kai a yankin Diffa da ke kan iyakar Chadi a Nijar. A cikin sanarwar an bayyana cewar, "Mun yi Allah wadai da wannan mummunar aiki na ta'addanci kuma muna mika ta'aziyarmu ga abokai da 'yan uwanmu na Nijar da gwamnatin kasar. Muna fatan rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa game da harin, Ma'aikatar Tsaro ta Nijar ta sanar da cewa kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta tayar da wani bam da aka dasa a baya a yankin Diffa yayin da wata motar sojoji ke wucewa.