Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Najeriya

Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Najeriya

Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da wata kungiya dauke da makamai ta kai kan makarantar kwana yayin da aka kashe wani dalibi, tare da sace dalibai da malamai sama da 40.

A cikin sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar an bayyana cewa,

"An gano cikin matukar damuwa cewa an yi garkuwa da malamai da dalibai sama da 40 yayin da dalibi daya ya mutu a wani hari da wata kungiya dauke da makamai ta kai a kan wata makarantar sakandaren gwamnati ta kwana a yankin Kagara da ke jihar Niger ta Najeriya.” 

A cikin sanarwar, an isar da ta'aziyya da fatan samun lafiya cikin gaggawa ga mutanen Najeriya da gwamnatinta.

Sanarwar ta kara da cewa "Mun yi Allah wadai da wannan mummunan harin kan daliban da ba su ji ba ba su gani ba. Muna fatan cewa daliban da malamai da suka bata za su iya haduwa da iyalensu da wuri-wuri." 


News Source:   ()