Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Chadi

Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Chadi

Turkiyya ta yi Allah wadai da harin ta'addanci da kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta kai a Chadi.

A cikin rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Waje ta fitar, an nuna bakin cikin samun labarin cewa sojoji da dama sun rasa rayukansu kuma mutane da dama sun jikkata a harin ta'addancin da kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta kai a yankin tafkin Chadi da ke kusa da iyakar Kamaru. 

A cikin sanarwar an kuma bayyana cewa "Muna Allah wadai da wannan aikin na ta'addanci, muna mika ta'aziyyar mu ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su, al’ummar kasar da kuma gwamnatin Chadi, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata." 


News Source:   ()