Albarkacin watan Ramadhan, Turkiyya ta bayar da taimakon kayan abinci na tan dubu 20 ga 'yan gudun hijirar Eritiriya da ke gudun hijira a wani sansani a gabashin Sudan.
Jami'in Hukumar Cigaba da Hadin Kai ta Turkiyya (TIKA) a Sudan Bilal Ozden a kokarinsu na rage radadi ga 'Yan gudun hijirar Eritiriya da ke Sudan sun hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu irin u Ethar da WeDCO tare da bayar da taimakon abinci a sansanin 'yan gudun hijira na Algirba da ke jihar Kesele.
Ozden ya kara da cewa, an bayar da kayan abinci mai yawan kilogram 20 ga iyalai dubu 'yan kasar Eritiriya da ke neman mafaka a Sudan.