Turkiyya ta soki kisan mutane da dama da aka yi a Najeriya

Turkiyya ta soki kisan mutane da dama da aka yi a Najeriya

Turkiyya ta soki harin ta'addancin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a Najeriya tare a kashe mutane sama da 40.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da rubutacciyar sanarwa inda ta bayyana cewar, Turkiyya ta yi matukar bakin ciki da samun labarin harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a yankin Zabarmari dake jihar Borno tare da kashe ma'aikata a gonar shinkafa su 43 da jikkata wasu da dama.

Sanarwar ta ce "Muna la'antar wannan hari. Muna Addu'ar samun jinkan Ubangiji ga wadanda suka mutu, da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Muna mika sakon ta'aziyya ga al'umar Najeriya da gwamnatin kasar."

 


News Source:   ()