Turkiyya ta soki harin ta'addanci da aka kai a Somaliya

Turkiyya ta soki harin da aka kai wa Rundunar Sojin Somaliya a Mogadishu Babban Birnin Kasar inda aka kashe sojoji dalibai 11.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar da cewa, Turkiyya na mika ta'aziyya ga kawa kuma 'yar uwa Somaliya sakamakon harin na ta'addanci.

Sanarwar ta yi Addu'ar samun jin kai ga wadanda suka mutu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

A sanarwar an kuma kara da cewa, Turkiyya za ta ci gaba da kasancewa tare da Somaliya da jama'arta.


News Source:   ()