Turkiyya ta soki hare-haren ta'addanci da aka kai a Mali, ta kuma kuma aike da sakon jaje da ta'aziyya ga jama'ar kasar.
Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce, Turkiyya ta yi matukar bakin ciki bayan samun labarin hare-haren ta'addanci da aka kai a sansanonin soji na garuruwan Boulkessi d Mondoro na Mali a ranar 24 ga Janairu tare da kashe sojoji 6 da jikkata wasu da dama.
"Muna la'antar wannan hari na ta'addanci. Muna mika sakon ta'aziyyarmu ga al'umar Mali da gwamnatin kasar. Muna fatan jin kan Ubangiji ga wadanda suka mutu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."
Ana yawan kai hare-haren ta'addanci a sansanonin soji na Boulkessi da Mondoro da ke Mali.
A watan Maris din 2020 an kashe sojoji 5 a harin da aka kai a sansanin Mondoro.
A shekarar 2018 ma an kashe sojoji 40 a hare-haren da aka kai a lokaci guda a sansanonin.