Turkiyya ta soki harin da aka kai a Mali

Turkiyya ta soki harin da aka kaiwa dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke aiyukan wanzar da zaman lafiya a Mali.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce,

"Turkiyya ta samu labarin mutuwar sojojin Ivory Coast 4 da jikkatar wasu 5 sakamakon harin ta'addancin da aka kai wa dakarun Majalisar Dinkin Duniya a yankin Timbuktu na Mali."

Sanarwar ta mika sakon ta'aziyya ga jama'ar Ivory Coast inda ta kara da cewa

"Muna sukar wannan hari na ta'addanci. Muna mika sakon ta'aziyya ga gwamnati da al'umar Ivory Coast. Muna mika ta'aziyya ga makusantan wadanda suka mutu da fatan sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."


News Source:   ()