Turkiyya ta soki hare-haren da aka kai a Najeriya

Turkiyya ta soki hare-haren da aka kai a Najeriya

Turkiyya ta soki hare-haren ta'addanci da aka kai a jihar Borno da ke Najeriya.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar da cewa, sun yi bakin ciki da samun labarin kai hare-haren ta'addanci a jihar Borno inda aka kashe mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.

Sanarwar ta ce "Muna mika ta'aziyyarmu ga gwamnati da jama'ar Najeriya kan mutanen da aka kashe a wannan hari na ta'addanci, muna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayyana cewa, an kashe mutane 10 tare da jikkata wasu 60 sakamakon fashewar wasu abubuwa a Maiduguri babban birnin jihar.


News Source:   ()