Albarkacin tunawa da ranar 15 ga Yuli Turkiyya ta raba tufafi ga marayu 251 a Kenya.
Ofishin jakadancin Turkiyya a Nairobi ne ya mika kayan taimako na tufafin ga marayun.
Jakadan Turkiyya a Nairobi Ahmet Jamil Miroglu ya ziyarci gidajen marayu da ke birnin inda ya raba musu kayan sawa da takalma.
Jakada Miroglu ya raba tufafi da takalman ga marayu 251 a cibiyoyi guda 2.
Ya ce, tsawon shekaru kungiyoyin Turkiyya ke bayar da taimako ga marayu, kuma Turkiyya za ta ci gaba da taimakawa masu rauni.