Turkiyya ta la'anci harin ta'addanci da aka kai wa dakarun kasar Mali inda aka kashe sojoji da dama.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce sun yi bakin ciki da samun labarin kai hari kan jami'an sojin Mali a kauyen Bouki-were na yankin Segou a ranar 14 ga watan Yuni, inda aka kashe sojoji da yawa.
Sanarwar ta ce "Muna la'antar wannan hari na ta'addanci. Muna Addu'ar samun jin kan Allah ga wadanda aka kashe, muna mika sakon ta'aziyyarmu ga 'yan uwa jama'ar Mali da gwamnatin kasar."
Bayan kai hari kan dakarun Mali a arewacin Bamako Babban Birnin Kasar a ranar 14 ga watan Yuni, an samu gawarwakin sojoji 24 daga cikin 44 da suka bata.
Rundunar Sojin Mali ta sanar da cewar bayan kai musu harin na kwantan bauna a yankin Segou da ke iyaka da Murtaniya, an samu gawarwakin sojoji 24 inda aka kbutar da wasu 8 daga hannun maharan.