Turkiyya ta la'anci harin ta'addanci da aka kai a Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce ta yi bakin cikin samun labarin cewar mutane da dama sun rasa rayukansu, wasu kuma sun samu raunuka sakamakon harin da aka kai da kuma arangamar da ta biyo baya a Mogadishu.
Sanarwar ta ce "Muna la'antar wannan hari. Muna mika sakon ta'aziyya ga gwamnatin Somaliya da 'Yan uwanmu jama'ar kasar. Muna fatan jin kan Allah ga wadanda suka mutu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."