Turkiyya ta kubutar da wani dan kasar Itali da aka yi garkuwa da shi a Kenya

Turkiyya ta kubutar da wani dan kasar Itali da aka yi garkuwa da shi a Kenya

Jami'an Leken Asiri na Turkiyya sun kubutar da wani dan kasar Italiya da aka yi garkuwa da shi a Kenya tare da kai shi Somaliya.

A watan Nuwamban shekarar 2018 ne aka yi garkuwa da dan kasar Italiyan Silvia Constanzo Romano mai shekaru 25 a yankin Chakama na Kenya inda aka kuma kai shi Somaliya, kuma daga baya mahukuntan Italiya suka bukaci jami'an Leken Asiri na Turkiyya da su kubutar da shi.

Sakamakon haka a watan Nuwamban 2019 jami'an na Turkiyya suka fara aiki na musamman don gano halin da Romano yake ciki.

Da fari sun fara amfani da jami'an leken aisir na Somaliya inda suka gano cewar Romano yana nan da ransa.

Sakamakon kyakkyawan aikin da jami'an Turkiyya suka yi an kubutar da Romano lafiya, kuma a makon da ya gabata an mika shi ga mahukuntan Italiya a Mogadishu Babban Birnin Somaliya.

Labaran da jaridun Italiya suka fitar na cewa Romano na aikin sa kai da wata kungiyar bayar da agaji mai suna Africa Milelel Onlus inda a wani lokaci ya ziyarci Kenya.

A Italiya an dinga yin maganganu game da samun 'yancin da Romano ya yi, sannan an ja hankali kan irin tasirin da Turkiyya ta ke da shi a yankin.


News Source:   www.trt.net.tr