Turkiyya ta aike da sakon ta’aziyya ga Najeriya bayan samun labarin cewa Boko Haram ta kai harin ta’addanci kan gwanon motocin sojoji a jihar Borno a jiya, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan sojoji 31.
A cikin sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar, an bayyana cewa “Mun yi Allah wadai da wannan mummunan harin na ta'addanci, kuma muna mika sakon ta’aziyya ga ’yan uwan wadanda suka rasa rayukansu da kuma kasar Najeriya baki daya.”
A jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, sojoji 31 sun mutu a wani hari da kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta kaiwa gwanon motocinsu a jiya.