Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Masar sakamakon hatsarin jirgin kasa da ya afku a kasar.
Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce, sun yi bakin ciki da samun labarin mutuwar mutane 11 sakamakon hatsarin jirgin kasa a gundumar Tuh ta jihar Kalyubiye.
Sanarwar ta ce "Muna fatan samun jin kan Allah ga wadanda suka mutu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Muna mika ta'aziyya da al'uma da gwamnatin Masar."
Ma'aikatar Lafiya ta Masar ta bayyana mutuwar mutane 11 da jikkatar wasu 98 sakamakon hatsarin jirgin kasa a kan hanyar Alkahira-Mansura.