Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Masar kan hatsarin jirgin kasa da ya afku a kasar.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya kan hatsarin da ya afku jiya a yankin Tahta na lardin Sohac da ke Masar, inda sama da mutane 30 suka rasa rayukansu kuma mutane da yawa suka samu raunuka.
A sakon an bayana cewa, "Muna fatan rahamar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu a wannan hatsari kuma muna addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Muna mika ta’aziyya ga Masar da al’umarta da iyalai da dangin wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin."