Turkiyya na ƙoƙarin ƙarfafa dantaka da ƙasashen nahiyar Afrika

Turkiyya na ƙoƙarin ƙarfafa dantaka da ƙasashen nahiyar Afrika

Ƙasar Turkiya ta zuba jari sosai a nahiyar Afirka a shekarun da suka gabata, abinda ya kai ga shugaba Recep Tayyip Erdogan ziyarar kasashe 31 da ke nahiyar har sau 50 a cikin shekaru kusan 20 da ya yi yana jagorancin kasarsa.

Wakilan kasashe 14 suka halarci wannan taron da ya gudana a Djibouti, wanda ya kunshi ministocin dake kula harkokin kasashen waje.

Ministocin sun hada da na kasashen Angola da Chadi da Comoros da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Masar da Equatorial Guinea da kuma Ghana.

Sauran sun hada da Libya da Mauritania da Najeriya da Sudan ta kudu da Zambia da kuma Zimbabwe.

Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan ya ce cinikayya tsakanin Turkiya da Afirka ya zarce dala biliyan 35 a shekarar da ta gabata, ya yin da zuba jarin Turkiya a Afirka ya zarce daga biliyan 7.

Kasar Turkiya ce ta 4 wajen sayarwa kasashen Afirka dake kudu da sahara makamai, baya ga horar da sojojin wasu kasashen dake nahiyar.

A  watannin da suka gabata, Turkiya ta yi kokarin sasanta rikicin kasashen Habasha da Somalia, baya ga kulla yarjejeniyar hakar ma’adinai da Nijar.

Turkiya na goyan bayan ganin Afirka ta zama mamba a kungiyar G20 da kuma yiwa kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya garambawul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)