Turkiyya ta sanar da cewar tana bibiyar al'amuran siyasa da ke afkuwa sau da kafa a 'yar uwa kuma abokiya Mali.
Game da kafa sabuwar gwamnati a Mali, Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da sanarwa cewa, ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya kai zuwa 'yar uwa kuma abokiyar kasa Mali, na kara tabbatar da yadda suke bibiyar al'amuran kasar sau da kasa.
Sanarwar ta tunatar da cewar a ranar 5 ga Oktoba shugaban rikon kwarya na Mali Bah N'Daw ya sanya hannu kan daftarin aiyukan gwamnatin wucin gadi da aka kafa.
Sanarwar ta ce "Muna sa ran bayan an nada Shugaban Kasa da Firaminista tare da kafa gwamnati, za a sake dawo da kundin tsarin mulki, za a magance matsalolin kasar ke fuskanta a yanzu tare da daukar matakan da suka kamata cikin hanzari. Yadda Majal,sar Dİnkin Duniya, Kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da Tarayyar Afirka suke ta kokarin ganin an tabbatar da komai ya tafi daidai a Mali abu ne mai dadi da faranta rai. Turkiyya za ta ci gaba da kasancewa tare da 'yar uwa kuma abokiyarta Mali a wannan yanayi."