Kotun dai ita ake kallo a matsayin mariƙa ɗaya da ta ragewa al’ummar ƙasar ta arewacin Afrika wajen samun adalci bayan da shugaba Kais Saied ya rushe kotun koli da majalisar alƙalan ƙasar a shekarar 2022 wanda ya kai ga korar tarin alƙalai daga bakin aiki.
Yayin zaman kaɗa ƙuri’a kan ƙudirin na jiya Juma’a, ƴan majalisa 116 cikin 161 ne suka nemi buƙatar yin garambawul ga tsarin dokokin zaɓen ƙasar.
Majalisar ta Tunisia da ke ci a yanzu, a shekarar 2022 ne aka zaɓe ta bayan da shugaba Saied ya rushe wadda aka zaɓa a farko, a wani yanayi da ɓangaren adawa ya kira zaɓen nasu da juyin mulki, lura da cewa kashi 11 na al’ummar ƙasar ne kaɗai suka kaɗa ƙuri’a a zaɓen.
Tuni dai wannan sabuwar doka ta haddasa zanga-zanga a sassan Tunisia ko da ya ke mahukuntan ƙasar sun gindaya matakan tsaro kasancewat an girke jami’a a lungu da saƙon babban birnin haka zalika an sanya shingaye a duk wata hanya da za ta kai ga zauren majalisar dokokin.
Duk da haka ɗimbin fararen hula ne suka yi dandazo a gab da shingayen riƙe da kwalaye masu rubutun da ke ala wadai da matakin majalisar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI