Tun a shekarar 2018 ne hukumomin ƙasar Kamaru suka kafa wasu sansanonin gyara tarbiyyar tubabbun mayaƙan Boko Haram a ƙasar.
Gwamatin kamarun ta shirya wuraren gyaran tarbiyyar a yankunan Meri da Mora kuma sama da mutum dubu 3 ne suka samu horo da koya musu sana’a a cikin wuraren da aka ware domin tubabbun mayaƙan.
Hukumomi sun ce za a saki mutum 600 a matsayin kason farko daga cikin mutum sama da dubu 3 na tubabbun mayakan Boko Haram ɗin domin su koma rayuwa kamar kowa tsakanin iyalansu da sauran alumma.
Wani tsohon ɗan ƙungiyar ta Boko Haram da ya miƙa wuya tun a shekarun baya, ya ce a yanzu a shirye yake domin ya koma cikin iyalansa ya ci gaba da rayuwa cikin salama.
Hukumomin ƙasar sun ce za su sanya ido sosai kan waɗanda aka yaye daga horon domin tabbatar da ganin shirin na gyara musu halayya ya samu nasara.
Shugaban dake kula da shirin a yankin arewacin Kamaru Oumar Cichair ya ce idan ba a yafewa mayaƙan da suka aje makamansu ba, to ba za su cimma burin da shugaban ƙasar ke da shi ba na tabbatar da zaman lafiya ba a ƙasar.
Wasu daga cikin tubabbun ƴan Boko Haram ɗin da suka shiga shirin ƴan asalin Najeriya ne, to amma sun amince su ci gaba da rayuwa a Kamaru domin gudun tsangwama idan suka koma ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI