Tsutsa mai abin mamaki da ke cinye sharar roba ta bayyana a Kenya

Tsutsa mai abin mamaki da ke cinye sharar roba ta bayyana a Kenya

Wannan ci gaba na zuwa ne a dai-dai lokacin da nahiyar Afrika ke fama da matsalolin muhalli da roba ta haddasa.

Binciken masanan na Kenya gano cewa wannan tsutsa ka iya cinye robo da ledodi da sauran tarkachen da ke lalata muhalli.

Binciken wanda aka gudanar da shi karkashin Fathiya Mbarak Khamis guda daga cikin manyan kwararru kan binciken lafiya ta ce, lokaci yayi da ya kamata a mayar da hankali wajen magance matsalar ta muhalli a nahiyar Afrika ba tare da jiran kowacce kasa ba.

A wata hira da sashen Hausa na RFI, Fathiya ta ce ana amfani da waɗannan nau’in tsutsotsi ne wajen kamun kifi ko kuma ciyar da kaji ga masu kiwon su.

Fathiya ta kuma kara da cewa don tabbatar da ingancin sakamakon binciken nasu, sun kwashe tsawon watanni suna baiwa tsutsar roba da kuma ledodi a matsayin abinci kuma a haka take cinyewa ta ci gaba da rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)