Tsohon shugaban hukumar zabe ya hada kai da 'yan tawaye

Tsohon shugaban hukumar zabe ya hada kai da 'yan tawaye

A halin yanzu kuma, shine jagoran gamayyar kungiyoyin ‘yan siyasa da kuma na ‘yan tawayen da ke neman kifar da gwamnatin.

Daga cikin kungiyoyin da ya hada kai da su, akwai wadda ke samun goyon bayan Rwanda ta M23.

Kungiyar ta tutsi ta tunkari manyan dakarun gwamnatin Congo da ke fagen daga, musamman a gabashin kasar, cikin shekaru 20 da ta dauka tana kai ruwa rana da su.

Mayakan kungiyar sun kwace garuruwa da dama, musamman wadanda suke kan iyaka, inda a halin yanzu kuma suka karkata akala zuwa Goma, biyo bayan wani gagarumin farmaki da suka kai, abin da ya tilastawa dubban mutane tserewa daga muhallansu.

Sai dai bayan kwace yankin na Goma, Nangaa ya ce yana da burin sake fasalta kasar.

Dan siyasa mai shekaru 54 ya tabbatar da cewa yana da masu goya masa baya, amma be yi cikakken bayani game da wadanda yake hulda da su ba.

A cewar wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, akwai manyan kungiyoyin masu dauke da makamai da ke taimakawa Nangaa, amma M23 ce kan gaba cikin masu mara masa baya.

Kasashen Faransa, Birtaniya, Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya, dukkanin su sun bukaci Rwanda da ta janye dakarunta daga Janhuriyar Congo.

Nangaa dai ya gaza musanta cewa yana samun goyon bayan Rwanda, duk da cewa ya ce Rwanda na goyon bayan kasancewar dakarun Burundi, abin da ake ganin shima ya haifar da fargabar yaduwar tashin hankali a sassan kasar.

Gwamnatin Rwanda dai ta jima tana musanta zarge-zargen da ake mata na taimakawa ‘yan tawayen, illa iyaka dai tana nanata cewa dakarunta suna aikin kare iyakokin kasarta ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)