Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Zuma ya shiga hannun jami'an tsaro

Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Zuma ya shiga hannun jami'an tsaro

An kama tsohon Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma da aka yankewa hukuncin daurin watanni 15 a kurkuku sakamakon kin yin biyayya ga kotu.

Sanarwar da aka fitar daga shafin Twitter na Asusun Zuma ta bayyana cewa, Zuma ya yanke hukuncin shiga kurkuku inda ya mika kansa ga jami'an tsaron kasar.

Kotun kolin Afirka ta Kudu ta bukaci Zuma da ya mika kansa a daren da ya hada ranakun 7 da 8 ga Yuli.

Zuma da ake ci gaba da tuhuma da zarge-zargen cin hanci, rashawa, damfara, kin biyan haraji da satar kudin gwamnati, ya ki zuwa kotu duk da bukatar hakan da masu bincike na gwamnati suka nuna.

Sakamakon bukatar da masu bincike suka gabatar watanni 4 da suka gabata, a ranar 29 ga Yuni kotun kolin Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin daurin watanni15 a kurkuku ga Zuma saboda kin girmama umarnin kotu.

A ranar 4 ga Yuli Zuma ya yi jawabi ga magoya bayansa a kusa da gidansa da ke Nkandla.

Zuma ya shaida cewa, ba ya tsoron shiga kurkuku, amma duba da shekarunsa idan aka kai shi kurkuku kamar an yanke masa hukuncin kisa ne.


News Source:   ()