Tsohon mataimakin shugaban kasar Kenya ya la'anci shugaban kasar William Ruto

Tsohon mataimakin shugaban kasar Kenya ya la'anci shugaban kasar William Ruto

Kotun ta ba da sanarwar ce ‘yan mintoci bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da nadin ministan cikin gida Kithure Kindiki a matsayin sabon mataimakin shugaban kasar.

Kindiki dai na hannun dama ne ga shugaba William Ruto ne.

Sai da Tsohon Mataimakin shugaban kasar ta Kenya Rigathi Gachagua ya yiwa shugaban kasar William Ruto wankin babban bargo, a yayin da ya bayyana shi a matsayin muggu wanda rayuwarsa ke cikin haɗari.

Gachagua wanda mambobin majalisar dattawan kasar suka tumbukeshi daga kujerarsa a ranar alhamis 17 ga watan Oktoba a kan wasu tuhume-tuhune da ake masa, ciki har da tunzura zangazangar kasar da barazana ga alkalai da gabar siyasa da dai sauran laifuka.

Gachagua mai shekaru 59 ya ci gaba da cewa an janye masa jami’an dake bashi tsaro tare da tilastawa daukacin hadimansa tafiya hutun dole.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar ya ce:

Na ɗimauce bisa yadda wanda na dafawa ya zama shugaban  kasa ya zama azzalumi, ban taba tunanin zai cutar dani ba” ya yi wannan bayani ne a yayin da yake ganawa da ƴanjarida.

Gachagua ya yi wannan jawabi ne bayan fitowarsa daga asibiti bisa wata ƴar gajeruwar jinya da ya yi a Nairobi babban birnin ƙasar bisa larurar ciwon ƙirji.

Ya ƙara da cewa:

“in har wani mummunan abu ya same ni ko iyalina to babu shakka ba zai rasa nasaba da samun hanun William Ruto a ciki ba, na yi zargin yunkurin halaka ni ta hanyar sanya min guba domin a kawar da ni”.

Babbar majalisar kasar ta ci gaba da kokarin tsige shi daga kujerarsa ne bayan da Lauyoyin Gachaguan suka gaza samun nasarar dage zaman daga kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)