Tsawa yayin zubar ruwan sama ta hallaka ɗalibai 14 da malaminsu a Chadi

Tsawa yayin zubar ruwan sama ta hallaka ɗalibai 14 da malaminsu a Chadi

Gwamnan lardin Ouaddai da haɗarin ya faru, ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa tsawa ce ta faɗa kan wata makaranta a yankin lamarin da ya kai ga rasa rayukan malamin da ɗalibansa 14.

Ƙaƙƙarfan ruwan sama haɗe da tsawa tuni ya haddasa gagarumar matsala ga yankin Tibesti a arewa maso yammacin Chadi wanda zuwa yanzu ya hallaka mutane 54.

A cewar mazauna yankin an shafe tsawon dare ana zabga ruwan hade da walƙiya mai ƙarfi baya ga tsawa wadda ta rusa gidaje da dama.

Daruruwan mutane ne ambaliya ta raba da matsugunansu a Chadi, lamarin da ya sanya gwamnatin ƙasar neman taimakon ƙasashe don agazawa waɗanda matsalar ta shafa bayan mutuwar mutane 70 a watan da ya gabata.

Wasu bayanai na nuna cewa ƙasar ta tsakiyar Afrika ta ga ruwan da ba ta taɓa gani ba a shekarun baya-bayan nan, hatta a yankunan da ba safai suka saba samun ruwa ba, lamarin da ya haddasa matsananciyar ambaliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)