Kimanin mutane 50 ne suka fake a majami'ar sansanin 'yan gudun hijira na Palabek da ke arewacin Uganda a yammacin ranar Asabar lokacin da wata mummunar guguwa ta afkawa yankin.
Mutane 14 ne suka mutu a lokacin da walkiya ta afkawa rufin karfen cocin na wucin gadi da suka hada da ‘yan mata biyar da kuma yara maza 9 masu shekaru tsakanin 14 zuwa 18, kamar yadda William Komech, jami’in gundumar Sao Paulo ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.
jana'izzar mutane a Uganda © AFP - STUART TIBAWESWA'Yan gudun hijirar galibinsu 'yan kabilar Nuer ne na Sudan ta Kudu.
"Gwamnati tana aiki tare da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) da sauran hukumomi don ba da agajin da ya dace ga wadanda suka tsira," Hillary Onek, ministar 'yan gudun hijira da shirye-shiryen Uganda, ta shaida wa AFP.
Birnin Kampala a kasar Uganda. © Michael Sugrue / Getty ImagesUganda ta fuskanci mace-mace masu nasaba da walƙiya a cikin 'yan shekarun nan. A shekarar 2011 ne, walkiya ta afkawa wata makarantar firamare, inda ta kashe dalibai akalla 18 da matasa tara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI