Hukumar kula da ƙaurar baƙi ta Majalisar ɗinkin duniya IOM ta ce cikin kwanaki 5 kaɗai da suka gabata, fararen hula dubu 1 zuwa dubu 3 ne suka tsere daga garin Umm Rawaba, gari na biyu mafi girma a arewacin yankin Kordofan da ke kudancin Sudan mai tazarar kilomita dubu guda daga El Obeid.
IOM ta ce a yankin na Kordafan kaɗai akwai mutane fiye da dubu 205 da yanzu haka suka rasa matsugunansu kuma galibinsu sun tsere ne a kwanakin baya-bayan nan, baya da yaƙin na watanni 20 ya tagayyara rayuwar jama’ar yankin.
A cewar IOM akwai mutanen da yawansu ya kai miliyan 11 da rabi waɗanda ke gudun hijira ciki kuwa har da wasu miliyan 2 da dubu 700 da suka tagayyara a baya-bayan nan, baya ga dubbai da suka mutu wasu kuma ke fama da matsanancin jinya a wani yanayi da ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa ke sanar da kawo ƙarshen aikinta bayan harin da ya sake hallaka mata jami’i guda.
Hukumar mai kula da ƙaurar baƙi ta ce wannan yanayi na zuwa a dai dai lokacin da yunwa ko kuma ƙamfar abinci ta afkawa yankuna 5 na Sudan dai dai lokacin da masana ke gargaɗin tsananin yunwa ya iya sake afkwa ƙarin yankuna 5 na ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI