Hakan na ƙunshe ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar.
A cewar Onanuga, Tinubu zai jagoranci taron hukumar haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11, tare da takwaransa shugaba Cyril Ramaphosa.
Sanarwar ta ce, za’a fara ne da zama na ministoci da manyan jami’an gwamnati daga ƙasashen biyu a zauren majalisar dokoki na Afrika ta Kudu a ranar Litinin, sannan a gudanar da ainihin taron a ranar Talata.
Tinubu da Ramaphosa za su tattauna kan batutuwa da dama da za su kawo ci gaban ƙasashensu, Afirka da kuma duniya baki ɗaya.
Sannan shugabannin za su ɗora kan batutuwan da suka duba lokacin haɗuwarsu ta ƙarshe ranar a watan Yunin da ya gabata, bayan rantsar da Ramaphosa karo na biyu a matsayin shugaban ƙasa, wanda hakan zai basu damar yin duba kan ci gaban da aka samu daga taronsu karo 10 zuwa yanzu.
Onanuga ya ce shugabannin za su rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama.
An samar da hukumar haɗin gwiwar tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu ne a shekarar 1999, domin yauƙaƙa alaƙa tsakanin kasashen biyu.
Hukumar na a matsayin wani dandamali na baje batutuwan da suka shafi alaƙar ƙasa da ƙasa, tattalin arziƙi, kasuwanci da zuba jari, tsaro da sauran abubuwa domin haifar da sakamako mai kyau tsakanin ƙasashen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI