Tinubu yace da taimakon Bankin raya kasashen Afirka na AfDB na Dala biliyan guda da miliyan 100, Najeriya za ta samarwa karin mutane miliyan 5 hasken wutar lantarki nan da karshen shekarar 2026, yayin da shugaban kuma ya ce a wannan shekarar za'a yi amfani da dala miliyan 200 wajen wadata mutane dubu 500 da wutar nan da karshen wannan shekarar ta 2025.
Shugaban ya kuma sanar da cewar suna shirin tabbatar da nasarar tallafin Bankin duniya na dala miliyan 750 domin inganta kananan tashoshin samar da wutar ga mutane sama da miliyan 16.
Tinubu ya jinjinawa shugaban Bankin duniya Ajay Banga da shugaban Bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina saboda gagarumin aikin da suka mayar da hankali a kai na samar da wutar ga mazauna Afirka.
Shugaban ya kuma bayyana cewar gamsuwar da masu zuba jari ke yi a kan irin matakan da gwamnatin sa ke dauka ya sanya 'yan kasuwa zuba jarin da ya kai dala biliyan 6 a bangaren samar da makamashin a shekarar da ta gabata.
Lokacin taron da ya gudana a Arusha, hukumar IFC ta ce zata zuba dala miliyan 70 domin taimaklawa 'yan kasuwa samar da wutar ta hanyar da ba ya gurbata muhalli.
Rahotanni sun ce Najeriya na bukatar jarin akalla dala biliyan 23 da miliyan 200 domin bunkasa bangaren samar da wutar domin wadata jama'ar kasa.
Taron ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka da dama, cikin su harda shugabannin Afirka ta Kudu da Ghana da Rwanda da Tanzania da mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Amina Muhammed da shugaban bankin duniya Ajay Banga da kuma shugaban Bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI