Taron zai mayar da hankali ne kan yadda za’a bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika da sauran batutuwa da dama, musamman kan batun ficewar ƙasashen Mali, Nijar da Burkina Faso daga ƙungiyar.
Haka zalika, taron karo na 66 zai kuma yi duba kan takunkuman da ECOWAS ta ƙaƙabawa ƙasashen Sahel ɗin 3, bayan juyin mulki da su ka yiwa fararen hula, yayin da basu halarci taron da aka fara gudanarwa yau Lahadi ba.
Shugabannin ƙungiyar ƙasashen ECOWAS yayin taronsu karo na 66 a Najeriya. © Nigerian PresidencyKana, za’a tattauna batutuwan da suka shafi ayyukan ta’addanci da ke ƙara ta’azzara a yankunan, tare da lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaron.
Ana sa ran mambobin ƙungiyar za su nazarci wa’adin da zasu bai wa ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin sojoji, domin mayar da mulki hannun fararen hula anan kusa.
A taron ECOWAS na ƙarshe, Tinubu ya naɗa shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye a matsayin mai sasanta tsakanin ƙungiyar da ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso domin su dawo cikinsu.
Daga bisani Faye zai gabatar da rahoton sulhun a gaban shugabannin ƙungiyar da zummar samun mafita nan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI