A watan da ya gabata ne Amurka ta gayyaci Sudan da kuma bangaren RSF da ke rikici da juna da su sake zama kan teburin sulhu don samar da mafita ta ƙarshe game da yaƙin da suke gwabzawa da juna.
Bayanai sun ce gwamnatin Sudan ɗin ta aike da tawagar ne a ƙarƙashin ministan ma’adanai Mohammed Bashir Abu Namo don wakiltar ƙasar a taron na ranar 14 ga watan da muke ciki.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa wakilan Amurka da kuma na Saudiyya ne suka tarbi tawagar a birnin Jidda.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ƙasashen duniya ke yunƙurin shiga tsakani don kawo ƙarshen wannan yaƙi da ya shafe kusan shekaru biyu ana tafka shi ba, amma har yanzu ba’a cimma nasara ba.
Bayanai sun ce yaƙin na Sudan kawo yanzu ya raba mutane sama da miliyan 2 da muhallan su, cikin su fiye da filiyan 1 da dubu 300 na samun mafaka ne a wajen ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI