
Wannan dai na zuwa ne, bayan da shugaban ƙasar ya sanar da cewa, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki a ranar 30 ga watan Nuwamba, duk da taƙaddamar 'yan adawa kan ƙarewar wa'adinsa a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya bayyana cewa, ganawar bangarorin, wadda ta ɗauki tsawon sama da sa'o'i biyu, ta gudana ne tsakanin shugaban jam'iyyar Labour ta Guinea-Bissau El Hadji Botche Cande, da shugaban jam'iyyar Social Renewal Party Félix Nandungue da kuma tawagar ECOWAS.
An rantsar da Embalo bisa wa'adin mulkin tsawon shekaru biyar, inda zai ƙare a ranar 27 ga Fabrairu, 2020.
‘Yan adawar ƙasar sun buƙaci abokan huldar Bissau da su daina daukar shugaba Embalo a matsayin halastaccen wakilin kasar, inda suke la’akari da ranar 27 ga Fabrairu a matsayin ranar da mulkinsa ya kawo ƙarshe.
Tawagar ECOWAS za ta ci gaba da zama a Guinea-Bissau har zuwa ranar Juma'a, a ƙoƙarin da take yi na samun matsaya, yayin da shugaba Embalo ke ziyara a kasar Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI